Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS) ta nuna alhininta da matukar damuwa akan kashe-kashen da ’yan bindiga ke ci gaba da yi a Jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato, Borno da sauran jihohin arewa.
Shugaban kungiyar ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan a wani zantawa da ya yi da ‘yan jaridu a ranar Asabar.
Shehin Malamin ya nuna damuwarsa matuka akan kisan kiyashi da ake yi a yankin Arewa maso gabas, da Arewa maso yamma.
Inda ya yi kira ga gwammatin tarayya cewa; kashe-kashen da ake yi ya yi yawa. Ya kuma ja hankalin gwamnati cewa; ko da rai guda ne wajibi ne gwamnati ta kare ballantana rayukan mutane masu yawa.