Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar ya karbi sama da mutane 142,000 daga jam’iyyar APC da sauran jam’iyyun adawa a Bauchi zuwa jam’iyar PDP
Daily Post ta ruwiato cewa, Atiku ya ziyarci jihar a karon farko bayan ya zama mai rike da tutar jam’iyyar PDP a zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka gudanar a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Kebbi Ya Baiwa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jigawa Miliyan 50
Ya samu tarba daga dubban magoya bayan jam’iyyar PDP, ‘ya’yan jam’iyyar APC da sauran jam’iyyun siyasar jihar wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a wani gagarumin taron da aka gudanar a filin wasa na garin Abubakar Tafawa Balewa dake jihar ta Bauchi.
Daga filin tashi da saukar jiragen sama na Bauchi Atiku ya zarce zuwa fadar Sarkin Bauchi domin ziyarar ban girma kafin ya wuce filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa inda dubban masu sauya sheka ke jiran halartarsa, ciki har da shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi mai ci Abubakar Suleiman, tsohon Mataimakin gwamnan jihar, Audu Sule Katagum da dan takarar gwamna, Faruk Mustapha wanda ya yanke shawarar sauya sheka zuwa PDP.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya taya wadanda suka sauya sheka murnar bude sabon shafi a fagen siyasarsu, inda ya ce ci gaba ne mai kyau da zai kawo wa jam’iyyar PDP nasara a babban zaben 2023.
” A yau mun zo ne domin murnar wannan gagarumin nasara da aka samu a jihar Bauchi. Zan iya tunawa a karo na karshe da nake nan, na ga irin ci gaban da jihar ta samu a dukkanin bangarori kuma an samu wannan ci gaba a karkashin gwamnatin Bala Mohammed na jam’iyyar PDP”.
“Yanzu kuna da gwamnati wacce kullum take ci gaba amma ya kamata ku kasance da wannan a ranku cewa siyasar Arewa na da nasa ba da jihar Bauchi, shi ya sa ba za ku yi wa siyasar Bauchi rikon sakainar kashi ba. A yau mun sake yin wani nasarar da muka samu na karin mutane zuwa jam’iyyar mu ta PDP, amma wannan ba shine yakin neman zaben mu ba, mun zo ne kawai don karbar ‘yan uwanmu da suka sauya sheka daga APC,” inji Atiku.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na kasa a lokacin da yake karbar jiga-jigan ‘yan takarar, ya ce Arewa maso Gabas ba ta samar da shugaban kasa ba amma a yau Allah ya zabi Atiku Abubakar wanda dan Arewa maso Gabas ne domin ya gyara duk wani kalubalen da ke damun al’umma da kuma hada kan al’ummar kasar nan.
Ya kuma ba da tabbacin cewa jirgin tawagar PDP na tafiya gaba, don haka kowa ya zo a tafi tare da shi.
Shi kuwa, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP cewa jam’iyyar a jihar za ta goyi bayan takararsa ta hanyar zuwa kowane lungu da sako domin tara kuri’un da za a kadawa jam’iyar PDP a zaben dake Tafe.
“Malam Atiku, mutanen Bauchi suna son ka, kuma sun san abin da za ka iya, sun yi imani da kai kuma sun yarda da mu. Muna tare a dunkule, za mu yi gangami ta hanyar PDP, za mu tabbatar mun je lungu da sako, kuma muna tabbatar muku da cewa ba za a wulakanta mu ba. A wannan karon dukkan al’ummar Bauchi da Arewa maso Gabas za su zabe mu, kuma za mu tabbatar da cewa kuri’un sun yi yawa”.
A WANI LABARIN KUMA: Yanzu-Yanzu: Bam Ya Tashi Wani Masallaci Dake Afghanistan
A sanyin safiyar Yau Laraba ne Wani abun fashewa ya tarwatse a wata Masallaci a Kabul Babban birnin kasar Afghanistan dake kusa da Ma’aikatar kula da harkokin cikin gida na kasar mai dauke da tarin jama’a.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito Kakkakin Ma’aikatar Abdul Nafi Takor na cewa, Masu ziyara ne ke amfani da Masallacin da kuma akasarin Ma’aikatan Ma’aikatar ta kula da harkokin cikin gida