Mambobin kungiyar Nuhu Ribadu Support Group da Tinubu Foundation a jihar Adamawa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Wannan dai na zuwa ne saura kwanaki biyar a gudanar da babban zaben kasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamba: Kotu Ta Amince da Belin Ɗan Uwan Gwamnan APC da Wasu Kan N2bn
Ko’odinetan gidauniyar Tinubu ta jihar, Suleiman Yarima ne ya sanar da sauya shekar a ranar Litinin a gidan gwamnati da ke Yola, a lokacin da ya jagoranci daruruwan ‘ya’yan kungiyar zuwa ga Gwamna Umaru Fintiri da wasikunsu na sauya sheka.
Suleiman ya bayyana cewa daukar matakin ya zama wajibi ne saboda irin gagarumin ci gaban da gwamnatin Fintiri ta yi a kowane lungu da sako na jihar.
Ya ce wasu daga cikin ‘ya’yan gidauniyar na daga cikin wadanda suka kafa jerin sunayen kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a jihar kuma ya sha alwashin cewa magoya bayansa za su zabi PDP.
Shima da yake jawabi shugaban kungiyar Nuhu Ribadu Support Group Alh Saidu Aliyu yace zasu tabbatar da zaben Fintiri da sauran yan takarar PDP daga sama har kasa.
Gwamnan ya godewa kungiyoyin bisa bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar PDP baki daya, ya kuma yi alkawarin ci gaba da gudanar da aikin a Adamawa.
A wanu labarin kuma, Mun Gyara Najeriya Fiye Da Yadda Muka Sameta A 2015 — Ministan Buhari
Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta ce Najeriya ta samu gagarumin ci gaba, fiye da na shekarar 2015 lokacin da jam’iyyar PDP ke mulki. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu ne ya bayyana hakan a lokacin da ya gabatar da shirin gidan talabijin na Najeriya NTA kai tsaye mai suna “Good Morning Nigeria”