Karamar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa ta sake bude makarantun da aka rufe saboda barkewar cutar kwalara a karamar hukumar.
Sakataren Ma’aikatar Ilimi na jihar Alhaji Sale Tata Alanjo ne ya sanar da hakan, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a jihar.
Ya ce Hukumar Ilimi ta ba da umarnin a gaggauta bude makarantu shida da aka rufe a karamar hukumar, sakamakon barkewar cutar kwalara a makarantun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an yan sanda sun kubutar da Sarkin Gargajiya a Jihar Niger
Alanjo ya ce, makarantun firamare da na sakandaren sun hada da na: Madamuwa, Zugo, Lafiya, Makarantar Firamare na garin Dolen Zugo , da Sakandaren dake garin Lafiya.
Ya kuma Kara da cewa, umarnin ya biyo bayan nasarar dakile yaduwar cutar a kauyuka hudun da aka yi.
Kazalika ya kuma shawarci iyaye, da su tabbatar yaran su sun koma makaranta.
Ya kuma yaba wa Gwamnatin jihar, na kananan hukumomi da kuma sauran hukumomin hadin gwiwa, bisa samar da magunguna don dakile yaduwar barkewar cutar a fadin jihar.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, Ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar mutane sama da 100, sakamakon barkewar cutar kwalara a kananan hukumomi goma sha tara na jihar.
Comments 1