By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa katinan zabe na dindindin guda 33,183 sun kammala a jihar Jigawa.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Dutse, mukaddashin sakataren gudanarwa na hukumar zabe mai zaman kata ta kasa INEC reshen jihar, Malam Ibrahim Idris, ya ce katinan PVC na wadanda suka yi rajista ne daga watan Yuni zuwa watan Disambar shekarar 2021.
Siyasar Kano: Shekarau, Sumaila, Rurum, Na Shirin Komawa NNPP Tare Da Sallama Da APC
Don haka ya yi kira ga wadanda suka cancanci kada kuri’a da su zo tare da bugu takardun sheda da aka basu a baya yayin yin rajistar don tantancewa da tattarawa domin karba cikin sauki.
Ya ce, “Ba a ba da izinin tattarawa ta hanyar wakili ba kamar yadda hotuna da yatsan hannun masu neman cancantar za su buƙaci a dauki hoton yatsun su kafin a tattara su.”
Idan dai ba’a manta ba a ranar 6 ga watan Mayu Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito hukumar zabe mai zaman kata ta kasa INEC ta fiyat da sabbin alkaluman masu rajista a ci gaba da yin rijistar masu kada kuri’a a fadin Najeriya (CVR) sun kai sama da miliyan 8,855,996 kamar yadda aka fitar a ranar 2 ga watan Mayu.
Hukumar tace cikakkun labaran na kwata hudu, mako na uku ya nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 5,415,619 ne suka kammala yin rajistar.
Jimillar mutane miliyan 2,379,063 ne suka yi rajista ta yanar gizo, yayin da miliyan 3,036,556 suka yi rajistar a ofisohi.
Wadanda suka kammala nasu sun hada da nakasassu dubu 45,412 (PWDs) da kuma matasa su kimanin miliyan 3,745,129.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta karbi aikace-aikace miliyan 15,789,718 domin sauya shekar masu kada kuri’a, da sauya katin zabe na dindindin (PVCs) da kuma sauya bayanan masu kada kuri’a.
A kididdigar da aka gudanar kimanin mliyan 8,330,813 maza ne, yayin da miliyan 7,458,905 mata ne.
Comments 1