Rundunar tsaro ta Civil defence reshen jihar Jigawa ta gudanar da wata jarrabawar gwajin kwakwalwa ga jami’an ta, da kuma tantance masu rike da mukamai, wanda hakan, umarnin ne daga babban kwamandan rundunar, Ahmed Abubakar Audi PhD, mni.
Bayan jarrabawar gwajin kwakwalwar, an kuma gudanar da atisayen wanda sashin kula da dabi’u na rundunar ya shirya, kuma an gudanar da shi ne cikin rukuni-rukuni domin kada a dakile sauran ayyukan hukumar. Wanda Shirin ya samu halartar ma’aikatan agaji daga shelkwatar hukumar ta ƙasa dake Abuja.
Da yake sanar da bude shirin na kwanaki biyu, kwamandan jihar Mustapha Talba (CC) ya bayyana dalilin da ya sa aka gudanar da atisayen wanda ya ce an yi shi ne da nufin tantance mizanin hankalin jami’an.
Har ila yau, yana daga cikin manufar shirya taron da nufin tabbatar da kwarewar su wajen amfani da makaman da ake basu.