Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Yusuf Zubairu bisa zargin kashe matarsa mai suna Fatima Hardo mai shekaru 23 da haihuwa.
An dai yi zargin ya kashe matarsa ne a lokacin da suke fada.
Lamarin wanda aka ruwaito ya faru ne a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2021, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Lawan Adam ne ya bayyanawa manema labarai haka.
A cewar wani ganau, Bulama Muntari-Ubale mai shekaru 65, mijin marigayiyar, wanda aka fi sani da “Allo”, ya yi amfani da sanda ya bugawa matarsa a kai a lokacin da aka samu rashin fahimtar juna, wanda a karshe ya yi sanadin mutuwarta. Ita ma wata mata da ta zo raba fada ta samu munanan raunuka, inji Bulama.
Adams yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan lamarin ya ce: “A yayin da aka tafka ta’asa, Yusuf Zubairu Wanda akafi Sani da Sallau, ya yi amfani da sanda ya bugi Fatima Hardo (wacce ta rasu a yanzu) a kai.
“Lokacin da wani mai suna Rabi Lawan, mai adireshi daya da inda lamarin ya faru, ta zo ta raba su, Yusuf Zubairu ya kuma yi mata mummunar rauni.”
Da samun rahoton, Adam ya ce an aike da tawagar ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru inda ma’auratan ke zaune a kauyen Baldi, a karamar hukumar Sule-Tankarkar ta jihar.
Ya bayyana cewa an garzaya da wadanda suka mutun zuwa babban asibitin Gumel inda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwar matar wanda ake zargin.
Ya kuma ce na biyun da aka jikkata an kai ta asibiti.
A halin da ake ciki, wanda ake zargin da kuma Sandar da ya yi amfani da ita wurin kashe marigayiyar, suna hannun ‘yan sanda, in ji kakakin rundunar.