Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya yabawa tsohon gwamnan jihar Sule Lamido da sauran gwamnatocin sojoji da na farar hula.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ya yaba musu din ne, bisa ci gaban jihar a cikin shekaru 31 da kafa ta.
Gwamnan ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake jawabi ga ‘yan jihar a bikin cikarta shekaru 31 da kafu.
Ya ce, “Na yi imanin yawancin mu za mu iya tunawa cewa shekaru talatin da suka gabata, lokacin da jihar ke hade da jihar Kano a wancan lokacin, ta kasance cikin tsarin ci gaban yankin tsakiya, wanda ba shi da mafi yawan cibiyoyi na gwamnati da abubuwan ci gaba.
KARANTA ANAN: Sojojin Da Suka Hallaka Shiek Goni Aisami Za’a Gurfanar Dasu A Kotun Fararen Hula
”Jama’a na ganin jihar a lokacin tana cikin halin kunci” Godiya ga dukkan shuwagabannin da suka mulki jihar tun daga kan mulkin soja, Kanar Olayinka Sule har zuwa yau, kowace gwamnati ta ba da gudunmawa ta kowace fuska wajen ganin jihar Jigawa da kuma inda take a yau”.
Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga malaman gargajiya da na addini da na jihar Jigawa bisa jajircewarsu wajen ci gaban jihar.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da yi wa jihar addu’ar zaman lafiya, ci gaba, da kuma ci gaban jihar da ma Nijeriya baki daya.
A wani labarin kuma: Japan, Da Isra’ila Zasu Hadu Don Samar Da Babur Mai Amfani Da Hasken Rana A Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejeniya da gwamnatocin Japan da Isra’ila kan kera babura masu amfani da wutar lantarki a kasar.
Yarjejeniyar wani mataki ne na farko ga Da zai kai ta zuwa wani yanayi na musamman, yayin da kasar ke kokarin rage fitar da iskar Carbon da kuma da ake da shi wajen kawo karshen matsalar sauyin yanayi.