By Abbas Yakubu Yaura
Jigo a jam’iyyar PDP kuma dan takarar Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a zaben shekarar 2019, Lawal Adamu Usman ya jajanta wa wadanda ‘yan bindiga suka kashe a harin da aka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a ranar Lahadin data gabata, sannan ya kuma yi alkawarin duba hanyoyin da za a kara tallafa musu.
Adamu, wanda aka fi sani da Mista LA, ya dora alhakin tabarbarewar tsaro a Kaduna a kan abin daya bayyana a matsayin rashin da’a da tauye hakkin da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Nasir Elrufai take yi.
Sannan yace yayin da yake tunanin hanyar da ta fi dacewa ta tallafa wajen rage radadin iyalan wadanda abin ya shafa, dole ne kowace al’umma a jihar Kaduna da sauran wurare su sabunta kudurinsu na hadin gwiwa wajen kokarin kawo karshen wadannan kashe-kashe na rashin tunani.
“Ina jin radadin wadanda suka rasa matsugunansu da kuma daukacin mutanen kauyukan Ruheya, Kauran Pawa, Marke da Idasu Gari da abin ya shafa,” in ji Adamu.
Da yake lura da alamun rashin nuna tausayi a bangaren gwamnati, Adamu ya bukaci addu’o’i da yawa domin neman gafarar Ubangiji, lura da cewa yawaitar munanan hare-hare da barnar da ake yi ya wuce fahimtar dan’adam kuma yana bukatar taimakon Allah.
Ya zargi halin gwamnati da jami’an tsaro da rashin kai farmaki a sansanin ‘yan fashi da makami da kuma jinkirin amsa kiraye-kirayen da wasu al’umma ke yi.
Sannan ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda suka rasu.
Comments 1