Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya tafi Landan ne domin ya huta, kamar yadda mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Ayo Oyalowo, ya bayyana.
Rashin halartar Tinubu a wajen taron yarjejeniyar zaman lafiyar da aka yi a ranar Alhamis din nan ya janyo ce-ce-ku-ce, inda aka rika yada jita-jitar cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ba shi da lafiya.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Amma da yake magana a wani shirin gidan talabijin na ARISE TV, Oyalowo ya ce, “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana Landan. Ba zai iya hutawa a Legas ba, ba za su bar shi ya huta ba. Yawancin lokaci yakan zo Abuja, kuma yanzu ba za su bar shi ya huta ba. Wannan mutumin yana aiki na tsawon sa’o’i 20 a cikin sa’o’i 24 a kowace rana. Don haka masu hankali sun ga ya kamata ya bar kasar domin mutane ba za su bar shi ya huta ba tunda yakin neman zabe na nan tafe.
KARANTA KUMA: Tinubu Ya Tafi Kasar Waje Domin Shirin Siyasar Da Mike kafa
“Gayyatar yarjejeniyar zaman lafiya ta zo ne bayan da Tinubu ya bar kasar. Ko da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima ba ya gari, dole ya bar abin da yake yi a Maiduguri.”
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ba kamar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba, wanda ya bayyana tafiyarsa zuwa Dubai a satin da ya rage kafin yakin neman zaben, tawagar Tinubu da a baya ta bayyana tafiyar tasa, ta yi shiru a wannan karon.
Lokaci na ƙarshe da rashin halartar Tinubu a taron jama’a ya jawo cece-kuce shi ne a taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da ya gidana a Legas.
A wani labarin kuma: 2023: Ba Mu Da Dan Takarar Shugaban Kasa, Inji Jam’iyyar ADC
Babban daraktan jam’iyyar African Democratic Congress ADC Sulieman AbdulAzeez, ya ce jam’iyyar za ta shiga zaben 2023 ba tare da dan takarar shugaban kasa ba.
Da yake magana da manema labarai a wani shiri a Kaduna ranar Juma’ar nan, ya ce an kori dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Mista Dumebi Kachukwu.