Rundunar sojin Bataliya ta dari da arba’in da hudu da aka jibge Mahadar Ariaria dake kan hanyar Enugu zuwa Fatakwal sun halaka yan bindiga sama da goma a yayin wata musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.
Wannan nasara na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani harin kwantan bauna da aka kai wa yan sanda tare da halaka su a yankin Abiriba dake karamar hukumar Ohafia na jihar.
Wadannan yan bindiga da aka yi kiyasin sun kai hamsain, sun far ma sojojin ne a wani gurin binciken ababen hawa dake mahadar ta Ariaria.
Wani shaidar gani da ido ya shaida cewa sun samu rahoton zuwan wadannan yan bindiga wanda hakan ya sa suka zauna cikin shiri.l
Yayin wannan musayar wuta wanda aka dauki tsawon miniti talatin ana yi an bindige sama mutum goma inda nan take suka ce ga garin ku yayin wasu daga cikin yan bindigar suka arce da gurbin alburushi a jikin su.