Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu a ranar Litinin ya rantsar da Farfesa Ikechi Mgbeoji a matsayin sabon Kwamishinan gona na jihar.
A yayin da yake jawabi a yayin rantsarwar a gidan gwamnati dake Umuahia, Gwamna Ikpeazu ya shawarci Kwamishinan da ya yi amfani da basirarsa da iliminsa wajen maishe da jihar matattarar ayyukan noma.
Har wala yau gwamnan ya shawarce shi da ya kalli mukamin da aka ba shi a matsayin wata dama da zai bai wa gwamnatin gudummawa domin cimma manufofinta na ci gaba. Sannan ya bukaci sabon Kwamishinan da ya yi aiki kafada da kafada da gwamnatin domin cimma nasarar kudurorin gwamnatin.
A jawabinsa, Kwamishina Mgbeoji ya bayyana gamsuwarsa da jindadinsa bisa wannan damar da aka ba shi domin yiwa jiharsa bauta da ba da na shi gudummawar wajen bunkasa jihar.