Jam’iyyar PDP Mai adawa a Kasar nan ta tara zunzurutun kudi da ya kai naira miliyan dari uku da hamsin da shida daga hannun masu sha’awar tsayawa takarar gwamnan Jihar Anambra su goma sha shida.
Ita Jam’iyyar ta PDP na saida takardar neman takara ne a kan kudi naira miliyan ashirin, sai takardar nuna sha’awar tsayawa takara a kan naira miliyan guda yayin takardar bin ka’idoji kuma take saida shi a kan naira miliyan biyar.
Rahotanni sun bayyana cewa yan takara goma sha shida maza da suka sayi fom din don fafatawa a zaben fitar da gwani sun batar da zunzurutun kudi har naira miliyan dari uku da talatin da takwas, inda ko wannen su ya kashe naira miliyan ashirin da shida.
Wani abin mamaki kuma dangane da yanayin tsarin da Jam’iyyar ta bi shine yadda aka saukaka wa yan takara mata suka biya naira miliyan shida kowannen su a matsayin kuɗin nuna sha’awar tsayawa takara da kuma kudin bin ka’idojin takara maimakon naira miliyan ashirin da shida.
Jam’iyyar ta ce ta saukaka musu biyan naira miliyan ashirin ne kowannen su bisa tsarin Jam’iyyar na karfafawa mata gwiwar shiga harkokin siyasa tsamo-tsamo.
A yanzu haka dai ana chan ana ci gaba da tantance yan takarar sha shida wanda taohon Gwamnan Jihar Kogi Idris Wada ke jagoranta.