Gwamnan Jihar Anambra Mista Willie Obiano ya yi Allah wadai da hare hare da aka kaiwa jami’an tsaro a Jihar ta Anambra.
Gwamna Obiano yana wannan Allah wadai ne yayin wani taro da Yan Jarida a Fadar gwamnatin Jihar Anambra wato Awka inda ya ce dole ne sai sun nemo duk wanda ke hannu wajen wannan aika-aika kuma ya fuskanci fushin hukama.
Ya ayyana ceqa Wannan hari da aka kai wanda ya sanadiyyar salwantar makaman jami’an tsaron wata kullalliya ce kawai don gurguntar da harkar tsaro a jihar.
Bisa ga wannan al’amari Obiano ya ce daga yanzu babu wanda za a sake bari ya yi amfani da gilashin mota mai duhu wato tinted ko kuma wanda ya rufe lambar motar shi.
A cewar shi za a girke jami’an tsaro da za su rika bin diddigin duk wata harkar barna a jihar don maido da doka da oda.
Wañnan hari dai da aka kai wa jami’an tsaron jihar wadanda suka hada da yan sanda da jami’an sintiri na Bijilanti an kai shi ne a ranar lahadin da ta gabata toh an yi nasarar dakilie shi daga bisani.