Gwamnan Jihar Binuwe Samuel Ortom ya ce ba maganar gudanar da zabe a shekara ta 2023 muddin aka ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a kasar nan.
Gwamna Ortom ya bayyana haka ne a gaban shugaban kasa Muhammadu buhari yayin wata ganawa da suka yi yau a fadar Shugaban kasa dake Abuja.
Gwamnan wanda ya kai wannan ziyara ga shugaban buhari ba tare da dan rakiya ba, sun tattauna ne kan matsalolin tsaro da suka addabi kasarw nan.
Ya kuma jinjina wa shugaba Buhari bisa yin Allah wadai da harin da aka mishi a gonar shi, to amma ya ce ba za a gudanar da zaben gaama gari na shekara ta 2023 ba muddin aka ci gaba da fuskantar matsalar tsaro.
Da yake karin bayani wa manema labarai bayan aganawar shi da Buhari, Ortom ya ce Kasar nan na zaune tamkar a kan kaya musamman a fuskar tsaro to amma babu wani katabus da aka yi a kan hakan.