Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a jihar Edo Henry Benamaisia, ya bayyana cewa mutane 149 ne suka mutu a wasu hadurran da suka faru a jihar a shekarar 2021.
Kwamandan sashin wanda ya bayyana hakan a ranar Talata a Benin yayin tattaunawa da Jaridar Daily Trust ya ce mutane 149 sun mutu a cikin hadurruka 235 da suka faru a fadin jihar.
Ya ce, “Jimillar fasinjoji 1,434 lamarin ya shafa a hatsaruka guda 235 a jihar, amma 149 sun mutu yayin da 521 suka samu raunuka a hadarin”.
Benamaisia ya ce an samu raguwar adadin mutanen da suka mutu tare da 13.9 a shekarar 2021 sabanin shekarar 2020 inda kasamu mutane 176 da suka mutu.
Ya ce motoci 432 ne suka haddasa hadurran da suka faru a fadin jihar.
Benamaisia ya Kuma danganta faruwar hatsarin da gudun wuce kima, ketare hanya ba bisa Ka’ida ba, tukin ganganci, tukin maye, rashin bin alamomin hanya da dai sauransu.
Ya shawarci masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar da su bi ka’idojin zirga-zirga domin su ci gaba da rayuwar su, yana mai ba da tabbacin cewa rundunar ba za ta amince da rashin da’a a kan hanya ba, kuma manufarsu ita ce rage hadurran a kan hanyoyin dake fadin kasar nan.