Osagie Ize-Iyamu ya samu nasarar zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo da ke tafe bayan ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.
Ize-Iyamu shi ne na hannun daman Shugaban Jam’iyyar APC da aka dakatar Adams Oshiomhole, a zaben da ke tafe ranar 19 ga watan Satumba.
Shugaban Kwamitin Zaben Dan Takarar kuma Gwamnan Imo Sanata Hope Uzodimna ya sanar cewa Ize-Iyamu ne ya lashe zaben bayan ya kayar da abokin karawarsa, tsohon mataimakin gwamnan jihar Pius Odubu.
https://dimokuradiyya.com.ng/ayyanannen-shugaban-apc-ya-soke-zaben-fidda-gwanin-gwamna-na-edo/