Babbar Jam’iya Mai adawa a Kasar Nan PDP reshen Jihar Edo ta bukaci Uwar Jamiyar da ta maida Takarar Shugabancin Kasa na Jamiyar ya koma Yankin Kudu Maso Kudu a shekara ta 2023.
Shugaban Jamiyar na Jihar Edo Tony Aziegbemi Wanda ya Mika wannan bukata yayin da yake zabtawa da Manema labarai Jan biking shi cika shekara guda Kan Mulki, ya ce an Yi Karan tsaye wa Jamiyar sa’in da aka haramta wa Tsohon Shugaban Kasa Good luck Jonathan wa’adi na biyu.
“Yayin da Kowa ya sani shekara ta 2023 ta Fara kunno Kai, Jam’iyyar mu ta PDP Mai albarka tana da Gawurtattun Mutane a shiyoyi shida na dadin kasar Nan wadanda za su iya karbe Mana Mulki cikin sauki, Na tabbata abin da aka Yi wa Tsohon Shugaban Kasa Good luck Jonathan Karan tsaye be yayin da aka haramta mishi wa’adi na biyu” Cewar Tony.