By Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan lafiya na jihar Ekiti, Dakta Oyebanji Filani, ya bayyana a ranar Alhamis cewa gwamnatin jihar ta kara sanya ido kan cutar zazzabin Lassa da nufin daukar duk wani wanda ake zargi da kamuwa da cutar da wuri.
Oyebanji, wanda ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan barkewar bazuwar cutar jini a jihar Nasarawa da kuma babban birnin tarayya, yace an tsaurara matakan sanya ido domin dakile barkewar cutar a jihar Ekiti.
Kwamishinan, a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Jihar Ekiti ta kara sanya ido kan cutar zazzabin Lassa bayan da aka samu bullar cutar a wasu jihohin’, ta sanar da jama’a cewa akwai yiwuwar cutar ta cigaba da yaduwa a wasu jihohin kasar nan.
Sannan ya kuma bukaci mazauna jihar Ekiti dasu lura da hatsarin dake tattare da cutar tare da bin matakan kariya kamar yadda NCDC ta tsara, gami da tabbatar da hanyar tsaftace muhalli a kowane lokaci.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kwamishinan na lafiya yace “Ku toshe duk ramukan gidanku don hana beraye shiga, ku rufe kwandon shara da zubar da sharar yadda ya kamata, adana kayan abinci kamar shinkafa, garri, wake, masara da dai sauransu a cikin kwantena da za’a iya lulluɓewa da murfi masu inganci sannan a guji shanya kayan abinci a waje ko a gefen titi, inda za a iya kamuwa da cutar,” in ji Kwamishinan.
Filani ya shawarci mazauna yankuna dasu guji shan magani kai tsaye a kowane hali, ciki har da lokacin da suka ga alamun zazzabin cutar Lassa da kuma zazzabin ciwon kai, ciwon makogwaro, raunin jiki gaba daya, tari, tashin zuciya, amai, zawo, ciwon tsoka, ciwon kirji a lokuta masu tsanani, zubar jini da ba a iya bayyanawa daga kunnuwa, idanu, hanci, baki da sauran buɗaɗɗen jiki.”
Sannan wani masanin likitan ya umurci ma’aikatan kiwon lafiya dasu ci gaba da kasancewa masu yawan tuhuma game da zazzabin Lassa, yayin da suke kiyaye daidaitattun ka’idoji don rigakafin kamuwa da cuta.
Yace “Dole ne a yi gwajin gano cutar cikin gaggawa ga duk wadanda ake zargi da kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro.Lokacin da RDT ba ta da kyau, ya kamata a yi la’akari da sauran abubuwan dake haifar da zazzabi, ciki har da zazzabin Lassa, “in ji kwamishinan.
A halin da ake ciki, Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya tace ta aike da wasiku ga jihohi kan bullar cutar zazzabin Lassa, kuma a halin yanzu an gano mutane akalla 436 da suka kamu da ita.
Comments 1