By Ishaq Dabai
Gwamnatin jihar Ekiti ta yi gargadi game da barkewar cutar a mai da gudawa tare da gano mutane biyar da ake zargi sun kamu da cutar a karamar hukumar Moba ta jihar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a Ado Ekiti jiya, ta hannun Kwamishinan Lafiya, Dokta Banji Filani, tace Ma’aikatar Lafiya ta karfafa sanya ido kan masu kwalara don daukar duk wani wanda ake zargi da laifin ya kamu da wuri don ya rage barkewar cutar.Filani yayi gargadin yiwuwar barkewar cutar a wasu kananan hukumomin jihar, inda ya bukaci mutane da su dinda tsaftar muhallansu.
Yace: “A ranar 19 gawatan Satumba, 2021, an samu rahoton bullar cutar kwalara guda biyar a Karamar Hukumar Moba ta jihar. Yace mun sami labari na al’umma da suka kamu da ita inda suka kai rahoto ga hukumomin kiwon lafiya na karamar hukumar waɗanda su kuma suka kai rahoto ga Ma’aikatar Lafiya ta jihar don yin kwakwkwaran bincike mai kyau.
“Dangane da haɗarin wannan barkewar dake taɓarɓarewa cikin sauri a duk faɗin jihar, Ma’aikatar Lafiya ta fara gudanar da binciken shari’a a duk ƙananan hukumomin jihar. An tura kungiyoyin sa ido na jihohi don tallafawa martanin barkewar cutar a matakin Kananan hukumomin.
“Waɗannan ƙungiyoyin suna ci gaba da bincike waɗanda ake zargi a cikin cibiyoyin kiwon lafiya, cibiyoyin kula da lafiya na yau da kullun da kuma tsakanin alummomi. Wannan ya yi dai dai da tsarin ayyukan gaggawa na farko da aka samar don magance yiwuwar barkewar cutar kwalara a jihar. ”
Ya kara da cewa: “Cutar kwalara cuta ce da za a iya hana cigabanta kuma ana iya magance ta mai saurin yaduwa ta hanyar cin abinci ko shan gurbataccen abinci ko ruwa. da yawan masu kamuwa da cutar kwalara na karuwa a lokacin damina kuma hadarin mutuwa daga cutar kwalara yana da yawa idan aka jinkirta kai mutum wurin magani.
“Don haka, yana da matukar muhimmanci a ziyarci cibiyar kiwon lafiya idan an ga alamun cutar kwalara kamar gudawa da amai.