By Ishaq Dabai
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa FRSC, reshen jihar Gombe tace akalla kimanin mutane 76 ne suka mutu a cikin hadarin mota 300 a jihar tsakanin watan Janairu zuwa Agusta.
Kwamandan hukumar, Mista Ishaku Ibrahim, shine wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a garin Lafiyawo da ke karamar hukumar Akko.
Ibrahim yace a cikin wannan lokaci da ake nazarin mutane guda 1,333 sun yi hadari daban daban, wasu 798 sun samu raunuka daban daban, yayin da guda 459 ba su ji rauni ba.
Ya kara da cewa an samu karuwar yawan hadarurruka tsakanin watan Janairu zuwa Agusta idan aka kwatanta da kididdiga ta shekarar 2020 a jihar.A cewarsa, tsakanin Janairu zuwa Agusta 2020, mutane 46 sun mutu a cikin hadari mota 191, wasu 545 sun sami raunuka daban daban, a yayin da guda 438 ba su ji rauni ba.
Kwamandan sashin ya alakanta karuwar hadurran a kan abubuwa daban daban, da suka hada da keta haddi na sauri, da rashin fitila mara kyau, tukin ganganci cikin dare, amfani da wayoyi yayin tuƙi da keta hanya.
Ibrahim yace za a kai kamfen na wayar da kan jama’a, wanda za a kaddamar ranar Juma’a, zuwa wuraren ibada da wuraren shakatawa na mota.