Wasu Yan bindiga sun kai farmaki izuwa Sakatariyar Karamar Njaba dake Jihar Imo a yau Litinin.
Maharan ba su kyale duk wani abin da suka samu a Sakatariyar kama daga Kofofi da tagogi da ababen hawa ne dai duk suka daidaita.
An kuma alaknta harin da na baya-bayan nan da ya wakana a shelkwatar Yan sanda da gidan yarin Wari fadar gwmantin jihar ta Imo.
Kazalika maharan sun yi kacha-kacha da shingen ababen hawa na sojoi dake hanyar Anacha da kuma wani shingen ababen hawan dake Ugwu Orji dukkanin su a karamar hukumar Wari ta Arewa.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji sun yi fargar jajin yayin da suka ga maharan inda suka gaggauata barin shingen da suke don kare kan su.
A harin da aka kai da sanyin safiyar yau din dai sama yan gidan yari dubu daya da dari takwas ne suka tsere daga gidan yarin Wari a jihar ta Imo.
Kuma tuni da ma aka kone ofishin yan sandan jihar kurmus sai toka.