Daga Khadija Muhammad Kano
Jihar Jigawa ce ta daya a fadin kasar nan wajen samar da ruwansha mai tsafta ga al’ummar ta.
Wani kwararre kan ruwansha da tsaftar muhalli na asusun unicef, Mista Bioye Ogunjobi ya sanar da haka a lokacin wani taron tattaunawa da kafafen yada labarai wanda ma’aikatar yada labarai ta tarayya ta shirya tare da hadin gwaiwar kungiyar tarayyar turai da ta Burtaniya da kuma unicef.
Ya ce kididdiga ta nuna sama da kashi tamanin da biyu na al’ummar jihar Jigawa na samun ruwansha mai tsafta.
Mista Bioye ya kara da cewa jihar Jigawa ita ce ta daya a arewacin kasar nan wajen hana bahaya a bainar jama’a, inda yanzu haka al’ummomi dubu uku da dari hudu da goma sha bakwai basa yin bahaya a bainar jama’a.
Daga nan ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar Jigawa ta amince da bada kudi naira miliyan dari biyu domin gina bandakuna ga sauran al’ummomin jihar da nufin magance matsalar bahaya a bainar jama’a.
Taron tattaunawar mai taken tsaftace Najeriya da muhalli da kuma shelar yin amfani da shadda ya hada kan wakilan kafafen yada labarai daga sassan kasar nan, inda aka tattauna kan gudummawar da zasu bayar wajen wayar da kan al’ummar ta.