Wakilinmu Ahamed Musa Gumel
Kamfanin samarda kayayyakin aikin gona na jihar Jigawa JASCO ya sayo takin zamani nauin NPK tan dari biyu akan kudi fiye da naira miliyan dari biyu.
Janar Manajan Kamfanin Alhaji Muhammad Lana ya sanar da hakan ga wakilinmu a ofishinsa.
Yace dama kamfanin yana da takin zamani tan dari biyu da ake sayarwa manoma a farashi mai sauki a wani mataki na habaka aikin gona.
Alhaji Muhammad Lana ya kara da cewar kamfanin ya kuma yi odar sayo kayayyakin gyaran tan tan daga kasar China domin kara habaka aikin gona ta hanyar amfani da kayayyakin noma na zamani.
Yace kari bisa wannan sun yi odar Karin injinan chasar shinkafa da alkama domin manoman jihar su rabauta da aikin gona.
Janar Manajan kamfanin na JASCO yacigaba da cewar kamfanin yana sayar da nauin kayayyakin aikin gona da suka hadar da takin zamani da tan tana da injinan chasar shinkafa da alkama da magungunan kwari a dukkannin shagunan kamfanin dake sassan jihar nan a farashi mai sauki.