Hukumar kula da shige da fice ta kasa, (NIS) ta naɗa sani Liman Kila a matsayin Kwanturolan shiyyar jihar Kaduna.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa kafin wannan nadin nasa, Sani Liman Kila, ya kasance babban jami’in kula da fasfo ne na hukumar, a Jihar Kano, kuma yana daga cikin waɗanda suka rabauta da Karin Girma na watan Mayun wannan shekara.
A yayin karin girman, jami’an hukumar kula da shige da ficen ta Kasa guda casa’in da takwas (98) ne, suka rabauta da karin girman, zuwa sabbin mukamai biyo bayan nasarar da suka samu a wani karin girma da aka yi wa manyan jami’an a watan Disamba na 2021.
DUBA WANNAN LABARIN: Kasashe Mambobin OPEC Sun Amince Da Kara Yawan Man Da Suke Samarwa
A wata sanarwa ta hannun Amos Okpu, Mataimakin Kwanturola, kuma jami’in hulda da jama’a na hukumar, ya fitar a ranar 28 ga watan Mayu, 2022, sanarwar na dauke da sunayen wadanda suka samu wannan karin girman.
Daga cikin su kuma akwai Sani Liman Kila, wanda shima likkafarsa ta daga, bayan la’akari da kwazon sa.
Sani Liman Kila Dattijo ne daya samu shaida daga al’umma daban daban, bisa riko da gaskiya da amanarsa.
Ana ganin cewa nadin nasa zuwa ga wannan matsayi kuma a jihar Kaduna zai taimaka sosai wajen kawo karshen wasu matsalolin dake da alaka da Shige da Fice.
Kazalika ana kyautata zaton zai taka muhimmiyar rawa wajen yaki da masu safarar muggan kayan laifi zuwa cikin jihar Kaduna Kamar yadda masu sharshi suka bayyana.