Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce jihar Kano ta zama wata matattara ta tara kowane dan Najeriya ko da kuwa wace kabila ya fito.
Kazalika ya ce jihar ta zamo wani wuri dake haɗa dangantaka a zama tsintsiya madaurin ki guda ba tare da nuna wani banbanci ba.
Osinbajo ya yi wannan kalamai ne a ranar asabar a birnin Kanon Dabo yayin bikin mika sandar girma qa mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15.
Yemi Osinbajo wanda ya wakilci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne, ya ce duk dan Najeriyar dake neman mafaka a fadin kasar nan to lallai idan ya shiga Kano zance ya ƙare.
Taron wanda ya gudana a filin wasa na Marigayi Sani Abacha dake kofar mata a birnin na Kano, ya samu halartar jiga-jigan mutane daga ciki da wajen jihar.