Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta samar da ruwan sha da ayyukan more rayuwa a fadin jihar.
Malam Garba Yusuf, Kwamishinan Albarkatun Ruwa ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai, a ranar Juma’a a Kano.
Ya ce saboda gudun hijirar da mazauna wasu garuruwa da ‘yan fashi da suka addabi jihohin da ke makwabtaka da Kano, ya taimaka wajen karuwar bukatar ruwa.
KARANTA ANAN: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jiga-Jigan Jam’iyyar APC a Kaduna
A cewarsa, lokacin da aka gina matatar ruwa ta Challawa, bukatar ruwa a Kano ya kai lita miliyan hudu a kowace rana, yanzu haka bukatar ta karu zuwa lita miliyan 200 a kowace rana.
“Ruwa wani bangare ne na rayuwa kamar yadda kuka sani, kuma dukkan halittu suna bukatar ruwa don su rayu, ita ma wannan ma’aikatar ita ce ke kula da aikin ban ruwa da kuma ba da gudummawa ga samar da abinci.
“Ya kamata mutane su fahimci cewa ruwa wani bangare ne na rayuwa wanda bai kamata a yi amfani da shi ba a wajen da bai dace ba, don haka dole ne mu yi kokarin gyara gurbatattun famfunan da muke da su,” in ji shi.
Yusuf ya ci gaba da bayanin cewa ma’aikatar ta na da sashen ban ruwa da madatsun ruwa da ke kula da ayyukan ban ruwa da kuma bayar da gudummawar gaske wajen samar da abinci a fadin jihar.
Ya kara da cewa an kafa kwamitin da zai wayar da kan jama’a don sanin cewa ana sayar da ruwa.
A wani labarin kuma: Wike: Abinda Atiku Ya Yi Min Alkawari A Landan
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana tattaunawar da suka yi da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, a wani taro da suka gudanar a birnin Landan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Atiku ya tafi Landan a watan da ya gabata don tattaunawa da Wike bayan Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC sun gana a Birtaniya.