Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana gamsuwar sa akan aikin da kasar Egypt za suyi, na samar da katafaran kamfani shinkafa wanda jihar Kano ce zata fi amfana da aikin a kasar nan.
Alhaji Aminu Ado Bayero CFR ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin shugabanin Gwamnatin Kasar Egypt dangane da aikin samar da wani kamfanin samar da shinkafa da zasu kafa a nan jihar Kano.
KARANTA ANAN: Joe Biden Ya Mayar Da Martani Ga Kudurin Trumph Na Tsayawa Takara
Mai Martaba Sarkin yace dangantakar dake tsakanin kasar masar da Nigeria musamman jihar Kano, dangantaka ce dake kara habaka tattalin arzkin Kano da kasa baki daya.
Ya ce masarautar Kano za ta bayar da gudunmawar data dace wajen ganin an samar da cigaban tattalin arzkin Kano da Nigeria baki daya.
Mai Martaba Sarkin ya kuma yabawa kasar ta masar bisa gudummawar da suke bayarwa wajen ilimantar da al’ummar a kasar nan.
A nasa jawabi Shugaban kamafanin Egta Alhaji Bashir Yusif Ibrahim yace, jihar Kano zata ci gajiyar samar da kamfanin shinkafa mafi girma a kasar nan wanda kasar masar zata samar a jihar kano.
Haka zalika a wani cigaban kuma Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin shugabanin hukumar zakka da Hubsi ta jihar Kano.
Tawagar hukumar sun je ne karkashin jagorancin shugaban majalisar limaman juma’a Shekh Muhammad Nasir limamin masallacin shekh Ahmadu Tijjani dake Kofar Mata a Kano.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Tarayya Ta Dage Kan Ba Za Ta Biya ASUU Ba ‘Ba Aiki Ba Biya’
Gwamnatin Tarayya ta dage cewa ba za ta biya malaman makaranta albashin aikin da ba su yi ba daidai da manufar ‘Ba aiki ba biya’.
Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tsokaci kan zanga-zangar da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ke yi kan biyan rabin albashin watan Oktoba.
Kungiyar ASUU da ta fara yajin aikin a watan Fabrairu, ta janye yajin aikin ne tun a watan Oktoba bayan da Honarabul Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai ya shiga tsakani.