Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin ministan wasanni da matasa na tarayya Mr Sunday Dare wanda ya kaiwa Gwamnan ziyara a ofishinsa dake gidan gwamnatin Kano.
A yayin ziyarar ne kuma ministan ya sanarwa da gwamnan cewa shine zai kasance mai masauki baki na gasar Wasanni ta matasa da za a gudanar nan gaba.
Da yake jawabi Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya godewa ministan bisa zabar jihar Kano, tare da ganin an gudanar da wasan a cikin ta wanda ya ce wannan shine karon farko da zata karbi bakuncin ta.
DUBA WANNAN LABARIN: Kwamishinar Muhalli da Gandun Daji ta Jihar Gombe ta sanar da Ajiye Muƙaminta
Ya kara da cewa jihar Kano ta kasance jihar mafi shahara wajen gudanar da wasanni, da suka haɗar da kwallon kafa, kwallon hannu, da sauran su, a shekarun baya da kuma yanzu.
Mr Sunday Dare ya ce sun zavi jihar Kano domin gudanar da wasannin duba da irin gudunmawar da Gwamna Ganduje ke baiwa bangaren wasanni, ga kuma zaman lafiya a jihar.
A cewarsa, wannan shine karon farko da gasar zata gudana a wajen jami’a, sabanin baya da ake gudanar da ita a daya daga cikin jami’o’in Nigeria.
A yayin ziyarar da ministan ya kawo Kano, Gwamna ya kasance yana tare da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Hon. Ali Haruna Makida, Kwamishinan matasa da wasanni Kabiru Ado Lakwaya da sauran su