To sai dai Rundunar yan sanda a jihar ta ce mutane tsra ne kawai yan bindigar suka yo garkuwa da su, kuma tuni ma aka kubutar da hudu daga cikin su.
An yi wa fasinjojin kwantan bauna ne a hanyar su ta dawowa daga ci kasuwa a Jibia wuraren karfe uku na y
Wanii shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa an sace fasinjoji 15 din ne cikin 18 da suke motar Kirar J5 inda suka cikita mutane ashirin Kenan yan bindigar suka yi awun gaba da su.
Wani Mai suna Aliyu Rumawa wanda al’amarin ya faru a idanun shi, ya shaida cewa yan bindigar sun fara harbin iska don firgita fasinjoji yayin sa suka durfafe su a mota.
“Fasinjoji 15 aka sace cikin 18 da suke motar, kuma suna dawowa ne daga cin kasuwa a garin Jibia, dukkanin su yan tireda ne”.
Ko da yake Kakakin Rundunar yan sandar jihar ta Katsina ASP Gambo Isah ya bada adadin mutanen da ya sha banban da wadanda Rumawa ya bada.
“Fasinjoji tara ne ba wai sha biyar ba aka yi garkuwa da su” abinda ya faru shine, wuraren karfe uku da rabi na yammaci wasu yan bindiga sun sace mutane tara a wata mota kirar J5″