Dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a jihar Kebbi, Alhaji Atiku Mai-Ahu; mataimakin dan takarar gwamnan, Barista Nafi’u Abubakar; da daukacin ’ya’yan jam’iyyar a matakin jiha, kananan hukumomi da mazabu, sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC. Kamar yadda Daily Psot ta ruwaito
A cewar wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na fadar gwamnati, Kwamared Abubakar Muazu Dakingari, dukkanin ‘yan takarar sanata na jam’iyyar SDP, da na majalisar wakilai, sai dan takara daya, da ‘yan takarar majalisar dokokin jihar duk sun sauya sheka.
KU KARANTA: Sam Emefele Bai Cancanci Zama Gwamnan CBN Ba – Inji Wani Gwamna
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Mai-Ahu ya mika wa Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Alhaji Abubakar Kana Zuru wasikunsu na janyewa tare da yaga katinsu na zama yayan jam’iyyar SDP.
Mai-Ahu da sauran wadanda suka sauya sheka sun shiga jam’iyyar APC ne a ofishin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, PCC, da ke Birnin Kebbi.
Ya sanar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a wajen liyafar, ciki har da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, cewa sun yanke shawarar shiga jam’iyya mai mulki ne bisa tabbacin cewa jam’iyyar APC ce kadai jam’iyyar siyasa da za ta iya kai Nijeriya ga tudun muntsira tare da bunkasa tattalin arziki.
Ya yi alkawarin cewa sabbin ‘yan kungiyar za su taka rawar gani wajen zagaya wa lungu da sako na jihar Kebbi domin zaburar da jama’a don kada kuri’a ga jam’iyyar APC a zaben na bana.
Da yake karbar wadanda suka sauya sheka, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Alhaji Abubakar Muhammadu Kana Zuru, ya yaba musu bisa yadda suka nuna jajircewa da kuma daukan matakin da ya dace na sauya shekar zuwa jam’iyya mai mulki, inda ya ba da tabbacin cewa za su samu ‘yancinsu da gata kamar kowane dan APC.
A wani labari kuma, Amurika Ta Musanta Goyon Bayan Wani Dan takara A Zaben Najeriya
Gwamnatin Amurka ta ce ba ta goyon bayan wani mutum ko dan takara ko jam’iyya gabanin babban zaben Najeriya.
Molly Phee, Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka kan Harkokin Afirka ce ta bayyana hakan a ranar Laraba, a Abuja.