Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu ya ce jiharsa za ta tabbatar tabbatar ta zama a sahun gaba wajen tabbatar da mafi karancin albashi ga ma’aikata wanda gwamnatin tarayya ta sanyawa hannu. GWamnan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a yayin da ya kai wata ziyarar ba za ta ga sansanin masu bautar kasa a jihar.
Sannan Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu ya amince da sabunta sansanin ‘yan bautar kasa wato NYSC na dindindin dake Dakingari a jihar ta Kebbi.
Gwamnan ya tabbatar da cewa; tuni ya ba da kwangilar sabunta sansanin ‘ya NYSC din, sannan za a magance matsalolin dake fuskantar sansanin musamman matsalar ruwa. Haka zalika ya ce; batun kara tsawon katangar ma, za a yi domin ya fi a yadda yake girma. Sannan ya tabbatar da cewa zai duba batun alawus dinsu, kuma jihar Kebbi za ta tabbatar ta zama a sahun gaba wajen tabbatar da mafi karancin albashi ga ma’aikata.
Ya ce batun zirga-zirga ma gwamnati za ta hada hannu da NURTW domin samar da ababen hawa ga masu bautar kasar, domin daukar su zuwa inda aka kai su a fadin jihar.