Shahararren malamin addinin musulunci a garin Ilorin na jihar Kwara Sheikh Shuaib AbdulSalam ya rasu.
Abdulsalam ya rasu ne a safiyar jiya sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita, yana da shekaru 68 a duniya.
Marigayi AbdulSalam, Mabiyin Sufanci ne, kuma Babban limamin garin Maraba ne, kana babban malamin darikar Tijjaniyya ne wanda yake da dimbin magoya baya tare da samun mutuntawa daga Akasarin al’umar jihar.
Daruruwan al’ummar musulmi ne suka halarci sallar jana’izar marigayin, wacce ta samu halartar manyan baki daga bangaren addini da na gwamnati.
Jami’an tsaro sun sha matukar wahala wajan sarrafa jama’a da cunkoson ababen hawa a Oniyangi, gidan marigayin dake kan titin Sarkin inda Kuma Nan ne aka yi sallar.
Babban Limamin Ilorin, Sheikh Mohammed Bashir Salihu ne ya jagoranci sallar.
Sakataren Kwamitin Kungiyoyin Musulmi (CMO) reshen Jihar Kwara, Sheikh Yusuf Murtadoh, ya bayyana shi a matsayin Musulmin kirki wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bada ilimi da kuma tasiri a rayuwar Musulmi.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana rasuwarsa a matsayin mai raɗaɗi, yana mai addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da Al-Jannah.