By Abbas Yakubu Yaura
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya tace ta yi rajistar karin sabbin wadanda suka kamu da cutar COVID-19, guda 1,368 a ranar Litinin, wanda ya kawo adadin wadanda aka tabbatar sun kamu a kasar zuwa 225,255.
Cibiyar ta bayyana hakan ne ta shafinta na yanar gizo da safiyar ranar Talata.
Inda ta bayyana cewa cutar ta COVID-19 ta karu a Legas a ranar Litinin wanda ya rage kwana hudu kafin zuwan ranar Kirsimeti, inda aka samu rahoton bullar cutar guda 844 daga cikin adadin mutane 1,368 na kasar da suka kamu.
Jihar Legas, wanda itace babbar cibiyar kwayar cutar a kasar, yanzu tana da adadin mutane 84,410, tare da masu cutar 3,500.
NCDC ta lura cewa birnin tarayya FCT ta sami adadin na biyu mafi girma a cikin mutane 209 wanda ya tabbatar da adadin masu cutar zuwa 25,070 har zuwa yau.
Sai jihar Oyo mai mutane 58, Abia mutane 51, Ondo-39, Ogun-30, sai Kaduna mai mutane 26, Delta-20, Akwa Ibom-17, Osun-15, da kuma jihar Ekiti mai mutane 12.
Kazalika jihar Anambra, da Zamfara sun samu mutane 7 masu dauke da ita kowanne su , Cross River, Kano, Kwara, da Ribas sun samu mutane 6 kowannen su, Bauchi 5, Gombe tana da mutane 3, sai jihar Plateau mutum 1 tal.
Cibiyar ta lura cewa adadin mutane 2,985 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar tun bayan barkewarta a kasar a ranar 27 ga Fabrairun shekarar 2020, yayin da mutane 211,660 suka warke kuma aka sallame su.
Sannan ta bayyana cewa kararrakin cutar da aka samu a kasar a yanzu sun tsaya a kan mutane 9,508 har zuwa ranar Litinin.
NCDC tace kasar ta gudanar da gwaje-gwaje kimanin 3,751,696 tun bayan da aka sanar da bullar cutar a shekarar 2020.
Kazalika ta kara da cewa cibiyar ayyukan gaggawa ta kasa da kasa (EOC), wacce aka kunna akan mataki na 2, tana ci gaba da daidaita ayyukan mayar da martani na kasa.