By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, a ranar Juma’a ya bayyana cewa jihar ta kasance a matsayi mafi girma a cikin jihohin da ke da masu damfara ta yanar gizo (intanet) da aka fi sani da “yahoo boys” a Najeriya.
Abiodun ya yi magana ne a filin Arcade, Oke-Mosan, Abeokuta yayin kaddamar da rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaron jihar, mai suna OP-MESA a ranar Juma’a.
Gwamnan ya koka da yadda masu damfarar yanar gizo kwanan nan suka gudanar da bikin karramawa a Abeokuta inda aka ba da kyautuka ga “mafi kyawun kutse da damfara.”
Abiodun ya ce “Jihar Ogun ce ke kan gaba a jerin sunayen yaran masu Yahoo.”
Gwamnan, ya ce ya shaida wa shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa, cewa ayyukan ‘ya’yan ‘yahoo’ sun yi yawa a jihar Ogun, saboda jihar ce ke karbar bakuncin manyan manyan makarantun a kasar da mukamin, ya ce shugaban EFCC ya amince.
Ya kara da cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf domin kafa kwamitin yaki da masu aikata laifukan kudi a jihar, da nufin fatattakar masu damfarar yanar gizo daga jihar.
Abiodun ya kuma shelanta yaki da sake bullar garkuwa da mutane, yana mai cewa ba su da gurbi a jihar.
“A kwanakin baya ina wani taro a Abuja dana halarta tare da Shugaban EFCC. Kuma cikin bacin rai ya ce da ni, ‘Jihar Ogun ce ke kan gaba a jerin ‘ya’yan Yahoo.’ Abin bakin ciki.
“Amma na ce masa, ban yi mamaki ba, domin jihar Ogun ce hedkwatar ilimi a kasar nan, kuma za ka tarar da irin wadannan yaran yahoo a cikin cibiyoyin ilimi, kuma ya yarda da ni.
“Ya ci gaba da ce mani ‘yan kwanakin nan, ‘ya’yan Yahoo sun yi bikin bayar da lambar yabo a Abeokuta, bikin bayar da kyautuka ga wanda ya fi kowa iya damfarar yanar gizo inda aka kama wasu daga cikinsu.”
Yayin da yake magana kan jigon OP-MESA, Abiodun ya ce an kafa ta ne domin yakar masu aikata laifuka a fadin jihar.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa za a zabo ‘yan kungiyar ne domin tabbatar da cewa sun samu horon da ya dace tare da tabbatar da sun jajirce wajen gudanar da aikinsu.
Gwamnan ya ci gaba da cewa kaddamar da wannan kayyakin da motoci goma sha biyar, da motocin yaki guda biyu da na’urorin sadarwa za a yi su ne a kowace shekara har sai an kai adadin da ake so.
A nasa jawabin, babban kwamandan runduna ta 81 na rundunar sojojin Najeriya, wanda ya kunshi jihar Legas da Ogun, Manjo Janar Lawrence Fejokwu, ya yabawa gwamnan jihar bisa sake farfado da wannan kayyakin tare da samar musu da kayan aiki.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayyana cewa, kayan wani misali ne na tallafi da zai ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, ya yi alkawarin yin amfani da kayan yadda ya kamata.
Alake kuma mai martaba sarkin Egbaland, Oba Adedotun Aremu Gbadebo a nasa jawabin, ya yabawa gwamnan bisa kokarin da ya yi wajen tabbatar da matsayin jihar a matsayin kasa mafi aminci a kasar nan.