Kungiyar Dattawan Arewa ta caccaaki matakin gwamnatin Jihar Ondo na gabatar da taken Kasar Oduduwa a matsayin cin fuska wa kasarnan.
Idan za a iya tunawa dai a ranar 6 ga watan Mayu ne Gwamnatin Jihar ta fitar da wata sanarwa mai dauke da sa hannun Babban Hukumar Kula da Harkokin Koyarwa ta jihar Tolu Adeyemi inda ta rarraba wa makarantun.
Sanarwar kuma ta ce tilas ne kuma makarantun su rika gudanar da taken kasar ta Oduduwa.
To sai ai cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa Hakeem Baba-Ahmad ya fitar yace lashakka wannan mataki cin fuska ne ga Najeriya da yan Najeriya.
Ya kara da cewa wannan mataki abin Allah wadai ne kuma bai kamata a yi sako-sako da shi ba domin barazana ce ga dorewar Najeriya tsintsiya madauri baki guda.