A ranar Larabar da ta gabata ce aka kama wasu maza biyu masu matsakaicin shekaru a yayin da suke kan aikin tono kawunan Kan Kawarwarki 16 da sassan jikinsu, a wata makabarta mai Nisan kilo mita daya 1, da hanyar Moniya zuwa Iseyin, na gari Iseyin a jihar Oyo.
Wadanda ake zargin dai su ne Alfa Yunusa Atikoko, da Wasiu Ajikanle.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen Odua People’s Congress (OPC) da Yoruba Revolutionary Movement (YOREM) ne suka kama mutanen a unguwar Alamole.
An kama su ne bayan sun tono gawarwakin tare da ajiye kokon kawunan a cikin buhuna.
Wani ganau ya shaida wa Majiyar Dimokuradiyya cewa an mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.
Rahotanni sun nuna cewa an samu korafe-korafe game da bacewar gawarwakin da aka binne a makabartar da hukumomi a makabartar suka kasa tantance gaskiyar lamarin.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Adewale Osifeso, ya ce nan ba da dadewa ba za a bayar da bayanan da suka dace kan batun.