Akalla ba a kasara ba gobara ta lamushe dukiya ta miliyoyin Naira a Babbar Kasuwar doya dake garin Namu na Karamar Hukumar Qua’anpan din Jihar Pilato.
Daruruwa Manoma da Yan Kasuwa da wannan ibtila’i ya ritsa da su na ci gaba da bayyana irin asarar da suka yi sakamakon gobarar.
Wasu daga cikin su sun roki gwamnati da ma masu ido da kwalli sa su dube su da idon rahama don basu ikon rage radadin Wannan al’amari.
Kuma tuni Sanata Mai Wakilatar Pilato ta Kudu inda wannan yanki yake Farfesa Nora Dadu’ut ta jajanta wa mutanen da abin ya shafa da ma al’ummar Namu jimlatan.
Ta Kuma bukaci gwamnati da ta sanya hannun ta cikin al’amarin don farfado da harkokin kasuwancin waɗan da suka gamu da wannan ibtila’i.