Daga: Comrd. Haruna Sardauna
Shirin tallafawa Manoma dubu-sha-daya (11000) a jihar Yobe, A yammacin yau Alhamis Hukumar Agajin Gaggawa na Kasa, dana Jiha karkashin jagoranci Dr. Mohammed Goje, sun kaddamar da Rabon kayayyakin Noma a Manoma 1200 dake gunduma 13 na fadin Karamar Hukumar Fune.
Kowani Manomi cikin mutum dubu-sha-daya (11000) da Hukumar NEMA tayi masa rigista, zai samu kaya kamar haka:
1. Buhun Taki 5.
2. Irin Gero, Dawa, Masara da Wake, kananan Buhu daya.
3. Injin Feshi guda 1.
4. Maganin Kwari guda Hudu.
A jawabin shugaban Hukumar Agajin Gaggawa na jihar Yobe, Dr. Mohammed Goje, yayi gargadi akan duk wanda ya saida wannan kaya zai fuskanci hukunci daga jami’an tsaro, ya kuma gargadi wanda suka amfana da shirin akan cewa, kar su kuskura, su dafa irin shukan da aka basu dan ci, irin shukan yana dauke da Sinadarin dazai cutar da Dan Adam.
Wannan shiri moriyane ta tsarin Gwamna Mai Mala Buni, na hadin guiwa da Gwamnatin tarayya, hukumomi da kungiyoyin agaji, domin tallafawa Manoma, a kananan hukumomi 17 dake fadin jihar Yobe.