Daga Muhammad Gambo Damaturu.
Gwamnatin Jihar Yobe ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta rage kason da take dauka daga kudaden shiga na kasar, sa’annan ta karawa Jihohi da kananan hukumomin kasar.
Sakataren Gwmnatin Jihar, Alhaji Baba Malam Wali ne ya yi wannan kiran, ranar a yau Juma’a 20 ga watan Agustan shekarar, 2021. Lokacin da yake bayani ga manema labarai, jim kadan bayan tattauna wa da tawaga daga hukumar kasabta kudaden shiga na Kasa, da suka kawo wa jihar ziyarar aiki, kan yunkurin yin gyaran fuska ga tsarin kasabta kudaden shiga na tarayya.
Baba Malam Wali, wanda ya jagoranci zaman tattaunawar a madadin Gwamnatin Yobe, a dakin taron ofishin sa, dake fadar Gwamnatin Jihar, inda ya ce, Akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta karawa Jihohi da kananan hukumomin kasar nan kaso, domin samun sukunin gudanar da ayyukan ci gaba a kauyuka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kutu taki amincewa da bukatar Shugaban kasar Kenya
“Duba da yadda jihohi da kananan hukumomin kasar ke kokarin gudanar da ayyukan ci gaba a yankunnan su, ya na da kyau, a kara musu kaso daga cikin kudaden shiga na tarayya”, inji Baba Malam Wali.
Tun da farko da yake jawabi, Shugaban tawagar, wanda kuma shine Komishinan dake wakiltar Jihar Yobe, a hukumar kasabta kudaden shiga na kasa, Alhaji Modu Aji Juluri ya ce, sun zo Yobe ne, domin tattauna wa da Gwamnatin jihar, akan yunkurin da Gwamnatin Tarayya ke yi, na gyaran fuska ga yadda ake raba Kudaden shiga na kasa Nigeria.
“Manufar wannan ziyarar itace, mu tattauna da Gwamnatin Yobe, kan kokarin gyaran fuska ga yanayin rarrana kudaden shiga tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohi, da Kananan Hukumomin kasar. Wanda daga bisani zamu rubuta rahoton bayanan da muka samu, musamman matsaya da aka cimma, mu mika shi ga hukumar, don yin abun da ya dace”, inji Modu Aji Juluri.
Taron ya samu halartar Komishinonin Ma’aikatun Filaye da Ma’adanai, Ma’aikatar Shari’a, Noma, Kiwon Lafiya, Yan Majalisa, da Shuwagabannin sauran ma’aikatu na jihar Yobe.