Gwamna jihar Yobe Mai Mala-Buni ya bayyana cewa; gwamnatinsa ta sayo tirakta 103 da tan 7,500 na takin zamani a wani mataki na rabawa manoman jihar dake kananan hukumomi 17.
Gwamna Mala-Buni ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Damaturu yayin da yake nuna kayan aikin. Ya kara da cewa za a mika wadannan kayayyakin ne ga manoman ne a farashi mai rahusa domin ganin gwamnatinsa ta bunkasa harkokin noma a jihar.
Gwamnan ya bukaci shugannin kananan hukumomi da su kula sosai wajen raba wa ka da a samu wasu su handame kayan ko a yi wani wajen da su.
Mala-Buni ya kuma yi umurni ga shugabannin da su tabbatar su yi adalci, ta yadda duka wadanda za su samu manoma ne.