Ana tuhumar tsohon gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari da yin sama da faɗi da wasu kuɗaɗe kimanin Biliyan 37.8 da gwamnatin tarayya ta bayar domin yin wasu ayyuka.
Da yake tattaunawa da manema labarai kwamishinan harkokin kuɗi na jihar Alhaji Rabiu Garba, yace gwamnatin jihar Zamfara ta gina manyan tituna a jihar wanda ta kashe kuɗaɗe kimanin Biliyan 47 daga shekara ta 2011 zuwa 2018, kuma gwamnatin tarayya ta dawo wa dawo da kuɗin da gwamnatin jihar Zamfara ta kashe.
Garba yace “Tsohon gwamnan yace kuɗaɗen da aka kashe kimanin Biliyan 47 yace gwamnatin tarayya ba ta dawo da su wanda nasan ba haka batun yake ba”.
“Amma da muka aikewa da ma’aikatar ayyuka ta gwamnatin tarayya cewar a dawo mana da wancan kuɗaɗen sai muka gano ashe an biya gwamna Yari tun a wancan lokacin”, cewar Garba.
Da aka yi ƙoƙarin jin ta bakin tsohon gwamnan, lamarin ya ci tura domin an kasa samunsa a wayar salula.
Da aka tuntuɓi hadiminsa kuma mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen jihar ta Zamfara Alhaji Sani Gwamna domin jin ta bakinsa ya bayyana labarin a matsayin “abun dariya”.
Gwamna yace kwamishinan bai san aikinsa ba, in har gaskiya ne maganar da yake an karkatar da kuɗin ai da hukumar EFCC zasu gabatarwa da ƙorafin domin dawo da kuɗaɗen.
Gwamna ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kai ƙara kotu in har iƙirarin da take yi gaskiya ne.