Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Adamawa ta ayyana kwanaki biyu a matsayin ranakun da babu aiki domin baiwa ma’aikatan gwamnati da ba su da katin zabe na dindindin damar zuwa karbar katin zabe.
Wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Dr. Edgar Amos, ya fitar, ta ce an amince da ranar Alhamis da Juma’a a matsayin ranakun da babu aiki domin baiwa wadanda har yanzu ba su yi rijistar zabe ba, su kuma karbi PVC din su.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/ku-ceci-najeriya-daga-rugujewar-da-take-yi-nwuche-ya-bukaci-majalissar-tarayya/
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, ya ayyana ranakun Alhamis 28 ga watan Yuli da Juma’a 29 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu, domin baiwa ma’aikatan da basu samu katin zabe na dindindin ba kafin wa’adin na ranar 31 ga watan Yuli, 2022, lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta za ta dakatar da aikin har sai bayan babban zaben 2023.”
Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa PVC za ta kasance babban abin lura a cikin shigar da yara a makarantu, samun kulawa a asibitoci da kuma aiwatar da wasu hakkoki da gata a jihar.
Kazalika, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, shi ma a ranar Laraba ya ayyana ranakun Alhamis da Juma’a 28 da 29 ga watan Yulin 2022 a matsayin ranakun hutu ga ma’aikata a fadin jihar.
A cewar wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai Muhammad Bello ya fitar, ya bayyana cewa, kwanaki biyun da aka ayyana an yi su ne domin baiwa jama’a da ma’aikatan gwamnati dama a jihar su shiga cikin ayyukan rajistar masu kada kuri’a da ake yi.
“Haka zalika, hutun kuma shi ne a baiwa shugabannin kananan hukumomi da kansilolinsu da ma’aikatan da suka amince su fita domin gangami da wayar da kan masu kada kuri’a su fita su yi rajista tare da karbar katin zabe na dindindin a jihar domin samun zama wani bangare na babban zaben kasar da ke tafe,” sanarwar ta kara da cewa.
A halin da ake ciki, kwamishinan kasa mai kula da shiyyar arewa maso gabas na INEC, Dakta Baba Bila, ya ce mutane miliyan 2.3 ne suka yi rajistar masu kada kuri’a da ake yi a yankin Arewa maso Gabas.
Bila ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan wani rangadin da ya kai a cibiyoyin rijistar a wasu kananan hukumomin jihar Adamawa.
Bila ya ce, “Halin aikin na CVR, zan ce an yi nasara a Arewa maso Gabas idan aka kwatanta da sauran shiyyoyin kasar nan.
“Aikin a Adamawa ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata, inda ya samu dimbin ‘yan kasar da ke son yin rijistar zabe a 2023.
“Duk da haka, shawarata ta gaskiya ita ce jama’a su daina yin rajista sau biyu domin hakan ba zai yi musu amfani ba, domin a karshe za a kawar da wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Kwamishinan zabe na INEC reshen jihar Adamawa, Kassim Geidam, wanda ya raka kwamishinan na kasa a yayin ziyarar, ya tabbatar wa wadanda suka koka da yadda ake tafiyar da rijistar cewa hukumar za ta duba kokensu.