Jikan Hambali Ya Taya Daukakin Al’ummar Jihar Katsina Murnar Shiga Sabuwar Shekara 2022
Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina a Karkashin Jam’iyyar APC a Shekarar 2019 Alhaji Garba Sani Dankani ya taya daukakin Al’ummar Jihar Katsina Murnar shigowar sabuwar shekarar 2022.
Alhaji Garba Sani Dankani na magana ne da Manema Labarai a ofishinsa dake Birnin Tarayya Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 9, Sun Kashe Dan Bindiga Daya A Jihar Kaduna
Kamar yadda Jikan Hambali ya bayyana, a dai-dai lokacinda aka shiga sabuwar shekara lokaci yayi da magoya bayanshi zasu kara jajircewa wurin fadakar da mutane akan manufofinshi na alkairi ga Jihar Katsina.
Tshohon Dan takarar Gwamnan ya bukaci magoya bayan nashi da suyi amfani da damar tarukan jama’a a duk inda suka samu kansu wurin Sanar da mutane waye shi da kuma manufofinshi.
Yace baya da wata akida da ta wuce taimakawa Al’ummar Jihar Katsina idan har Allah ya bashi damar shugabancin jihar.
A sabili da haka Jikan Hambali ya bukaci Al’umma akan kada suyi kasa a gwuiwa wurin mara baya ga sahihan yan takara dake kaunarsu
Comments 1