By Abbas Yakubu Yaura
Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Ahmad Danbaba, ya rasu.Jaridar Daily Trust ta tattaro daga wani makusancin dangin sa, Alhaji Buhari Sarkin Tudun Jabo, ya ce ya rasu ne a yau a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.
Ya shaida wa manema labarai cewa, “Muna cikin kaduwa sosai, don haka ba zan iya yin cikakken bayani game da marigayin ba a halin yanzu. Muna shirye shiryen kai gawar mamacin Sokoto domin yi masa jana’iza.
“Za a yi jana’izarsa a jiharsa ta haihuwa, Sakkwato, a yau. Babban rashi ne ba ga danginsa ba, Jihar Sakkwato, dama ga daukacin al’ummar kasa baki daya.”