Gwamnan Jahar Kogi Yahaya Bello ya sami lambar yabo daga babban bankin duniya bayan ya zuba kudade dala milyan 4.63.
Babban bankin duniya ya nuna jindadinsa baya saka makudan kudaden da ya samar karkashin hukumar Nigeria Erosion and Watershed Management Project (NEWMAP). Kamar yadda Jaridar Punchnews ta ruwaito a shafinta
A wani sakon takadda wanda Shugaban bankin Shubham Chaudhari ya nuna cewa wannan salon mulkin adalci ne.
KARANTA:- Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnatin Yobe ta samu tallafin bunkasa dajin Jakusko Nasari
Kamar yadda bankin duniya ya bayyana ya kara tsawaita damar kulla Yarjejeniya kan wasu ayyukan na daban da sauran wasu jahohi biyo bayan babbab abunda gwamna Yahaya Bello yayi.
Kamar yadda jawabin ya kunsa a takardar ” “Na rubutu wannan sako ne don nuna jindadina bisa makudan kudaden da ka turo zuwa reshen Plateu na dala miliyan 4.63.”
“Bisa wannan gagarumar aiki ka sanya bankin tsawaita wa’adin rufe kulla Yarjejeniya kan wasu ayyukan daga 30 June 2021 zuwa 30 June 2022. Wannan na nuna mulki na adalci da gwamnatin ka take gudanarwa.”
“Zuba kudaden ya saura jahohi dake da bukatar kammala sauran ayyukansu su kammala, sannan Kuma Jahar Kogi na kokarin cigaba da sauran ayyukansu.”
“Za kuma mu cigaba da wai-waiyen gwamnatin ka don ganin ka kammala sauran ayyukan naka.”
“Muna yin amfani da wannan dama wajan mika godiyan mu da jindadin fatan wannan sako zai kara maka kaimi.”
A wani labarin
Saraki na kokarin tare mu wajan tabbatar da laifinsa, EFCC a KotuSaraki na kokarin tare mu wajan tabbatar da laifinsa, EFCC a Kotu
A ranar Laraba ne Hukumar EFCC tacewa babban Kotu Najeriya dake Abuja Abubakar Bukola Saraki na kokarin hana mu tabbatar da laifinsa.
Jagoran hukumar ta EFCC kan binciken Saraki, Chile Okoronkwo ya bayyanawa mai Shari’a Awunli Chikere lokacin da kungiyar kare hakkin Dan adam ta gabatar da tsohon shugaban Yan majalisu Abubakar Bukola Saraki a Kotu.
Hukumar ta EFCC a shekarar 2019 tace, za ta gabatar da abunda Abubakar Bukola Saraki yake samu tun daga 2003 har zuwa 2011 lokacin yana gwamnan Jahar Kwara.
Hukumar ta ruwaito cewar an kwace wasu gidajen shi dake Ikonyi a Jahar Legas a lokacin.
Hukumar yada labarai ta Najeriya ta ruwaito cewar, a ranar goma ga watan May shekarar 2019 an gabatar da karar Abubakar Bukola Saraki a gaban Kotu da takadda mai lamba FHC/ABJ/CS/507/19 da FHC/ABJ/CS/508/19 gaban mai Shari’a Taiwo Taiwo inda yake tuhumar hukumar ta EFCC.
Alkali Taiwo mai Jagorantar shari’ar ya cigaba da sauran karar da hukumar ta EFCC ta gabatar tare da sauran masu kare su guda biyar, inda yace musu su cigaba da binciko hujjoji akan karar, sannan aka dage shari’ar zuwa wani lokacin.
An baiwa Abubakar Bukola Saraki dama ne bayan mai kareshi ya gabatar da wata takarda a ranar 14 ga watan May a shekarar 2019.
Wadanda suke cikin shari’ar sun hada da Attorney General of the Federation (AGF), Inspector-General of Police (IGP), State Security Service (SSS), Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) and Code of Conduct Bureau (CCB) da masu kare shari’ar na 1st, 2nd, 3rd, 5th sannan da 6th.
Kotun dai ta sanar da mai kara da wanda ake kara dasu bar shari’ar.
Sai dai Alkalin hukumar ta EFCC yace da akwai takarda da zai gabatarwa kotu.
Alkalin ya cigaba da cewa, a kwai wata kotu wadda Taiwo ya Jagoranta tace masu kara su cigaba da nemo hujjoji akan karar.
Sai dai hakan ya jawo hana masu karar guda hudu kaddamar da aikinsu har na tsawon shekaru biyu.
Okoronkwo, yace zai cigaba da bada hadin Kai ga kotun a duk lokacin da aka gayyace shi, ya kumayi kira ga Kotu da ta kori karar.
Chikere yace za’a dakatar da karar nan ba da dadewa ba, yanzu an dage zaman zuwa 7 ga watan Octoba don cigaba da Shari’a.