By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta sanar da dakatar da ayyukanta na kwanaki biyu na wucin gadi wanda ta fara a ranar Talata.
Shugaban hukumar NATCA, Abayomi Agoro, ya shaidawa jaridar Dimokuradiyya cewa, an dakatar da yajin aikin ne domin bada damar ganawa da Darakta-Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya, Musa Nuhu.
Agoro ya shaida wa wakilinmu a ranar Laraba cewa taron zai gudana ne da karfe biyu na rana a Abuja sannan kuma sakamakon taron shine zai tabbatar da matakin da za a dauka na gaba.
Jami’an kula da zirga-zirgar jiragen sama yace sun hana zirga-zirgar tashi ta mintuna 20 na zirga-zirgar jiragen cikin gida a manyan filayen tashi da saukar jiragen sama guda hudu a Legas, Abuja, Fatakwal, da Kano don matsawa bukatar da suke ta neman samar da walwala ga mambobinta da dai sauransu.
Jiragen saman cikin gida sun gamu da cikas a ayyukansu na yau da kullun a ranar Talata yayin da NATCA ta fara aikin masana’antu kafin ta dakatar da hakan.
A halin da ake ciki, Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya ta tabbatar wa masu amfani da sararin samaniyar da sauran jama’a cewa, sararin samaniyar na Najeriya ya kasance cikin aminci ga zirga-zirgar jiragen sama marasa inganci da tattalin arzikin matafiya.
“Mun kuma yi nadamar duk wata matsala da aka samu tun daga farko,” in ji Manajan Daraktan NAMA, Fola Akinkuotu, a cikin wata sanarwa.