Kungiyar KWallon Kafa ta Barcelona dake kasar Spaniya ta atbbatar da cewa dan wasan tsakiyra ta Phillipe coutiinho ya tafi kasarsa ta haihuwa wato Brazil don duba raunin da yake fama da shi a gwiwa.
Dan wasan dan shekara 28 rabon shi da buga wa Barcelona wasa tun watan Disambar shekarar bara sakamakon raunin da ya samu a kokon gwiwar shi a karawar barcelona da Eibar cikin gasar Laliga.
Duk da cewa wannan jinya ta jima a jikin Coutinho, jaridar Marca ta ruwaito cewa ciwo yana tashi ne a jikin wanda ake ganin kamar ma ba zai sake fafta wasa ba a wannan kaka.
Wannan ya sa ala tilas bayan gwagarmaya ana jinyar dan wasan a kasar Qatar barcelona ta yanke shawarar tura shi kaasar shi ta haihuwa wato Brazil ganin cewa abin ya ci tura.
Wannan ne yanayi mafi muni da coutinho ya shiga tun bayan hadewar shi da Barcelona daga Liverpool, inda ake ganin kwalliya fa ta kasa biyan kudin sabulu bayan kawo shi Nou Camp kan farshin Pam Miliyan 140.