Ministan sufuri na kasa, Chibuike Amaechi ya bayyana cewa za a ci gaba da jigilar fasinjoji da jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja kafin Babbar Sallah. Ministan ya tabbatar da hakan ne a cikin sanarwar da shafinb Ma’aikatar Sufurin ta wallafa a Twitter. Inda ta tabbatar da furucin ministan.
A yau ne dai ake sa ran gudanar da gwajin sabbin jiragen ƙasan da aka kai Kaduna, sai dai za a fara amfani da su ne idan an ci gaba da jigilar.
Ministan ya buƙaci hukumar gudanarwa ta jirgin ƙasar ta ɗauki matakai na daƙile yaɗuwar annobar cutar korona kafin buɗe jigilar jiragen.