Wani jirgin saman kasar Sin dake dauke da mutane akalla 133 yayi hadari a tsakanin wasu tsaunika dake kudancin lardin Guangxi
Jirgin kirar Boeing 737-800 na dauke da Fasinjoji 123 ne da kuma Ma’aikata 9, kamar yadda Hukumar Kula da Filayen sauka da tashin jiragen Samar kasar CAA ta tabbatar.
Sai dai har kawo hada wannan rahoton, hukumar ta CAA ba ta bayyana adadin wadanda suka rasa rayukansu ba sanadiyar hadarin, ko kuma musabbabin afkuwar hadarin.
Amma Rahotanni sun nuna cewa, an tura jami’an aikin Ceto wurin da lamarin ya faru, yayin da bishiyoyi a yankin suka kama da wuta sanadiyar hadarin jirgin, kana ana kyautata zaton cewa babu wanda yarayu daga cikin mutanen dake cikin jirgin.